Home Top Ad

Nmandi kanu ko ya mutu?

Share:

- Emanuel Kanu wanda ya kasance kani ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, yace iyalan sa sun dukufa wajen neman shugaban kungiyar da iyayen sa tun makonni biyu da suka gabata amman ba'a ci nasarar ganin sa ba
- Rundunar soji ta karyata labaran dake cewa shugaban kungiyar yana a hannun su
- Yan majalisa sun tuhumi sanata Enyinnaya Abaribe bisa tsayawa da yayi a matsayin sheda ga Kanu
Emmanuel Kanu kani ga shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, yayi kira ga hukumomin sojoji da su saki gawar shugaban kungiyar masu fafatukar kafa Biyafara (IPOB) idan ma kashe shi suka yi.
Emmanuel yayi kiran ne a ranar Talata, 26 ga watan Satumba, a lokacin da yake magana kan cigaba da bacewar shugaban kungiyar na IPOB bayan farmaki da rundunar soji ta kai wa gidajensu a jihar Abia a ranar 14 ga watan Satumba.
“Walau sojojin sun kama shi kokuma sun kashe shi a lokacin da suka kaiwa gidan shi hari. Idan kama shi suka yi, su sako shi ga yan sanda, kuma idan kashe shi suka yi, su nuna mana gawar sa saboda ganin shi na karshe ya kasance jin kadan kafin rundunar ta kai farmakin ne,” a cewarshi a yanda jaridar The Cable ta wallafa.
Emmanuel Kanu ya bukaci gawar shugaban kungiyar IPOB
Yace iyalan su na cigaba da neman Kanu da iyayen sa na tsawon makonni biyu ba tare da nasarar ganin su ba tun lokacin da aka kai farmaki a gidansu.
KU KARANTA KUMA: An nada ma IPOB kungiyar ta’addanci saboda kalamun batanci – Ministan tsaro
Emmanuel ya bukaci hukumomin kasashen waje da su sa baki don ganin rundunar soji ta fitar da iyayensa da babban yayanshi.
Duk da haka, rundunar soji ta cigaba da karyata zancen cewa Kanu yana a hannun ta.
A lokacin da aka kira daya daga cikin layukan da ma’aikatan Operation Python Dance suka sake wa jama’a, muryar da ya daga kiran yace Kanu baya a hannun rundunar soji.

No comments